1 John 2

1ʼYaʼyana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don kāriyarmu-Yesu Kiristi, Mai Adalci. 2Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.

3Mun san cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa. 4Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa: 6Duk wanda ya ce yana rayuwa a cikinsa dole ne yǎ yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi.

7Abokaina ƙaunatattu, ba sabon umarni nake rubuta muku ba sai dai tsoho, wanda kuke da shi tun farko. Wannan tsohon umarni shi ne saƙon da kuka riga kuka ji. 8Duk da haka ina rubuta muku sabon umarni; ana ganin gaskiyar umarnin a cikinsa da kuma ku, domin duhu yana shuɗewa haske na gaskiya kuwa yana haskakawa.

9Duk wanda ya ce yana cikin haske yana kuma ƙin ɗanʼuwansa ashe a duhu yake har yanzu. 10Duk wanda yake ƙaunar ɗanʼuwansa, a cikin hasken yake rayuwa ke nan, kuma babu wani abin da yake cikinsa da zai sa yǎ yi tuntuɓe. 11Amma duk wanda yake ƙin ɗanʼuwansa, cikin duhu yake yana kuma tafiya cikin duhu ke nan; bai ma san inda za shi ba, domin duhun ya makantar da shi.

12Ina rubuta muku, ʼyaʼyana ƙaunatattu,
domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa.
13Ina rubuta muku, ubanni,
domin kun san shi wanda yake tun farko.
Ina rubuta muku, samari,
domin kun ci nasara a kan mugun nan.
Ina rubuta muku, ʼyaʼyana ƙaunatattu,
domin kun san Uba.
14Ina rubuta muku, ubanni,
domin kun san shi wanda yake tun farko.
Ina rubuta muku, samari,
domin kuna da ƙarfi,
maganar Allah kuwa tana zaune a cikinku,
kun kuma ci nasara a kan mugun nan.

Kada Ku Ƙaunaci Duniya

15Kada ku ƙaunaci duniya ko wani abin da yake cikin duniya. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa. 16Gama duk abin da yake na duniya-shaʼawace shaʼawacen mutuntaka, shaʼawar idanunsa da kuma taƙama da abin da yake da shi yake kuma yi-ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya. 17Duniya da shaʼawace-shaʼawacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah zai rayu har abada.

Gargaɗi A kan Magabcin Kiristi

18ʼYaʼyana ƙaunatattu, wannan ita ce saʼa ta ƙarshe; kuma kamar yadda kuka ji cewa magabcin Kiristi yana zuwa, ko yanzu ma magabtan Kiristi da yawa sun zo. Ta haka muka san cewa saʼa ta ƙarshe ta iso. 19Sun fita daga cikinmu, ai, dā ma can ba namu ba ne. Don da a ce su namu ne, da sun kasance tare da mu; amma fitarsu ya nuna babu ko ɗaya daga cikinsu da yake namu.

20Amma ku kam, kuna da shafewa daga wurin Mai Tsarkin nan, kuma dukanku kun san gaskiya. 21Ina rubuta muku ba don ba ku san gaskiya ba ne, aʼa, sai dai don kun san ta, kun kuma san cewa babu yadda ƙarya za ta fito daga gaskiya. 22Wane ne maƙaryaci? Ai, shi ne mutumin da yake mūsun cewa Yesu shi ne Kiristi. Irin wannan mutum shi ne magabcin Kiristi-ya yi mūsun Uban da kuma Ɗan. 23Ba wanda yake mūsun Ɗan, saʼan nan yǎ ce yana da Uban; duk wanda ya yarda da Ɗan yana da Uban a cikinsa ke nan.

24Ku lura fa cewa abin da kuka ji daga farko, yǎ ci gaba da kasance a cikinku. In kuwa ya ci gaba da zama a cikinku, za ku kasance a cikin Ɗan da kuma cikin Uban. 25Wannan shi ne abin da ya yi mana alkawari-har ma rai madawwami.

26Ina rubuta muku waɗannan abubuwa ne game da waɗanda suke ƙoƙari su sa ku kauce. 27Game da ku kuwa, shafan nan da kuka karɓa daga gare shi tana nan a cikinku, ba kwa kuma bukata wani yǎ koyar da ku. Amma kamar yadda shafan nan tasa tana koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba—yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.

ʼYaʼyan Allah

28Yanzu fa, ya ku ʼyaʼyana ƙaunatattu, sai ku ci gaba a cikinsa, domin saʼad da ya bayyana mu iya tsaya gabagaɗi babu kunya a dawowarsa.

29In kun san cewa shi mai adalci ne, to, kun dai san cewa duk mai aikata abin da yake daidai haifaffensa ne.

Copyright information for HauSRK